IQNA

19:31 - March 24, 2017
Lambar Labari: 3481341
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri dangane da addinin muslunci a jami’ar Carleton da ke birnin Ottawa a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, shafin jaridar jami’ar Carleton ta (The Charlatan) ta bayar da rahoton cewa, a yau an fara gudanar da wani shiri a jami’ar da nufin kara samar da masaniya a tsakanin dalibai da kuma bincike kan addinin musulunci.

Wannan shiri ya kunshi jawabai da kuma amsa tambayoyi daga dalibai da kuma ma’aikata da ma jamar da suka halarci wurin danbgane da abin da ya shafi muslnci, inda aka gayyato malamai da masana addini domin su bayar da amsoshi.

Baya haka kuma shirin ya kunshi raba kwafin kur’ani da aka tarjama a cikin manyan harsuna, domin bayar da su ga jama’a kan su karanta da kansu domin ganin abin da kur’ani ya kunsa.

Shirin na da nufin kara fadada fahimtar jama’a dangane dangane da kyamar muslunci ta ke ci gaba da yaduwa a kasar, inda hakan zai taimaka wajen rage kaifin kyamatar musulmi da ake yi ta hanyar fahimtar addininsu cewa bas hi ne ta’addanci ba.

Wannan shiri zai zai ci gaba da gudana daga nan har zuwa ranar Litinin mai zuwa, inda ake ci gaba da karbar baki a wurin da ake gabatar da shirin.

3585524

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Carleton ، Ottawa ، Canada ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: