IQNA

23:46 - March 29, 2017
Lambar Labari: 3481357
Bangaren kasa da kasa, jami'ar birnin bagdad ta kasar Iraki ta dauki nauyin shirya gudanar da wani taro na ku'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, jami'ar birnin Bagadaza ta dauki nauyin shirya wani taro na kur'ani mai tsarki tare da halartar manyan jami'an gwamnati da kuma wasu daga cikin masana

Bayanin ya ce wannan taro ya shafi dakarun sa kai ne da ke taimaka ma dakarun tsaro a kasar wajen yaki da 'yan ta'adda tare da tsakake birane daga mamayar 'yan ta'addan takfiriyyah a kasar.

Babbar manufar shirya wannan taro dai ita ce kara karfafa gwiwa dakarun sa kan dangane da lamari da ya shafi ubangiji, ta hanyar jin ayoyin kur'ani da kuma tunatar da su muhim,amncin aikin da suka dauka domin gudaar da shi a tafarkin Allah madaukakin sarki.

Dakarun sa kan da suka halarci wurin wannan taron, sun gudanar da karatun kur'ani mai tsarki, tare da sauraren bayanai daga malamai kan muhimamncin aikinsu wanda yake a matsayin jihadi a tafarkin Allah, domin kuwa suna kare kasarsu da ul'ummarsu da kuma addinin musulunci, daga sharrin mutanen da suke bata sunan addinin muslunci a iduniya tare da cutar da al'ummar musulmi da sauran al'ummomin duniya.

3586029
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: