Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin aljarida.com cewa, a ci gaba da gudanar da taron baje kolin littafai na kasar Tunisia, an nuna wasu daga muhimman abubuwan da suka hada da kyallen dakin Ka’abah a wurin.
Bayanin ya ce daya daga cikin masu gudanar da aikin sakar kyallen dakin ka’abah Muhammad Al-taum shi ne ya zo da kyallen, inda yake yin sakar a gaban jama’a, wanda kuma wannan kyallen da yake sakawa na daga cikin wanda za a saka a kan Ka’abaha lokacin aikin hajji mai zuwa.
Taron baje kolin kasar Tunisiya wanda shi ne karo na talatin da uku da ake gudanar da shi, yana daga cikin muhimman tarukan baje kolin littafai a kasashen musulmi, domin kuwa madaba’antu daga kasashen duniya suna halartarsa.
Ana bangaren shugaban kasar ta Tunisia ya bayyana jin dadinsa matuka dangane da ci gaban da aka samu a wannan karo fiye da na sauran lokutan da suka gabata a taron baje kolin littafai na duniya akasar.