IQNA

23:41 - June 02, 2017
Lambar Labari: 3481574

Iyalan Wadanda Mahukuntan Bahrain Ke Tsare Da Su Na Cikin Damuwa

Bangaren kasa da kasa, iyalan mutanen da mahukuntan Bahrain suka kama Durraz na cikin damuwa saboda rashin sanin makor danginsu.

Iyalan Wadanda Mahukuntan Bahrain Ke Tsare Da Su Na Cikin Damuwa

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da da jaridar Wasat ta kasar Bahrain ta yi da iyalan mutanen da masarautar kasar ta kame a garin Durraz, sun nuna damuwa matuka a kan rashin sanin halin da danginsu suke ciki.

Jami’an tsaron masaratar Bahrain tare da ‘yan banga na wannan masarauta, sun kaddamar da farmaki da manyan makamaia a unguwar Durraz da ke kusa da birnin mana, domin tarwatsa jama’a da suke zaman dirsha a kofar gidan babban malamin addini na kasar.

Jami’an tsaron tare da ‘yan banga sun kame mutane 286 wadanda a ‘yan kwanakin bayana jin duriyar inda wasu daga cikinsu suke inda ake tsare da su, amma a halin yanzu babu duriyar ko daya daga cikinsu, lamarin da ya kara tayar da hankulan danginsu.

3605713


captcha