IQNA

An Gudanar da Gasar Kur’ani Ta Somaliland

23:44 - June 12, 2017
Lambar Labari: 3481604
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar kur’ani ta shekara-shekara a yankin Somaliland tare da halartar makaranta da maharrdata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar The National cewa, an gudanar da wannan gasa ne kamar yadda aka saba yia kowace shekara a cikin watan azumin Ramadan mai alfarma.

Ahmad Muhammad Mahmud Silaniyo shugaban yankin Somaliland shi ne ya kirkiro wannan gasa, kuma a ke ci gaba da gudanar da ita a garin Hargisa fadar mulkin yankin na Somaliland.

Abdulhamid Sheikh Mustafa Adam matashi dan shekaru 13 da haihuwa, shi ne ya zo na daya awannan gasa ta bana, kuma ya samu kyautar mota da kudin zuwa aikin hajjin bana a matsayin kyautar lashe gasar.

Tun a cikin shekara ta 2010 ne dai Silaniyo ya kirkiro wannan gasa, wadda ta samu karbuwa atuka atsakanin al’ummar yankin na Somaliland.

Wannan gasa dai ita ce babban taron da aka fi yin a addini a wannan yanki wanda yake samu halartar malamai, da kuma gabatar da bayanai na addini domin fadakar da jama’a.

Tun a cikin shekara ta 1991 ne yankin Somaliland ya sanar da ballewa tare da kafa kasa mai cin gishin kanta, amma dai har yanzu kasashen duniya ba su amince da ita ba a hukumance.

3608861


captcha