Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jaridar
wadda take mayar da hankali wajen bayar da labaranta dangane da siyasar
kasashen larabawa da yankin gabas ta tsakiya, ta habarta cewa, majiyoyin
diplimasiyyar sun tabbatar mata da cewa an gudanar da zaman ne a birnin
Alkahira fadar mulkin kasar Masar a makon da ya gabata.
Jaridar ta kara da cewa, an gudanar da wannan zaman a sirri ne a tsakanin wakilan Isra'ila, Saudiyya, Amurka, UAE, Masar da kuma Jordan, kuma zaman yana da dangantaka ne da batun yankin Palastinawa na zirin Gaza, da ke karkashin ikon kungiyar Hamas, wadda sukkanin kasashen da suka halarci zaman suke kallonta a matsayin kungiyar ta'adanci.
Zaman ya gudana ne a cikin sirri matuka, a kan haka babu cikakken bayani kan abubuwan da aka tattauna dalla-dalla, amma bisa ga dukkanin alamu akwai wani boyayyen lamari da ake kitsawa a kan yankin na Gaza, da Isra'ila take ci gab ada killace shi tsawon shekaru.