IQNA

Taron Tarjamar Kur'ani Ta Duniya A Kasar Morocco

17:38 - July 03, 2017
Lambar Labari: 3481665
Bangaren kasa da kasa, za agudanar da taron tarjamar kissoshin kur'ani da littafai masu tsarki a karo na biyar a kasar Morocco.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa , ya nakalto daga shafin linguistic.org cewa, wannan taro zai gudana karshen wannan shekara tare da halartar masana daga bangarorin musulmi da kiristoci da kuma yahudawa.

Wannan taro dai shi ne irinsa na biyar da za a gudanar a matsayi na kasa da kasa tare da halartar dukkanin bangarori na wadannan addinai guda uku da aka saukar daga sama da suka kunshi bayanai da kisoshi na al'ummomi da suka gabata.

Daga cikin kishoshin da ake fitarwa har da na annabawa da kuma al'ummomin da suka rayu a lokutansu da yadda aka karbi kiran annabawa da kuma yadda wasu suka juya musu baya da irin abin da ya faru da su, da ma wasu daga cikin kisoshi na hikima da ilmantarwa da ke cikin kur'ani mai tsarki da sauran littafai da aka saukar daga sama.

A taron masana musulmi da yahudawa da kuma kiristoci da suke son a kara fadada fahimtar juna tsakanin mabiya wadfannan addinai duk za su gabatar da laccoci da kuma mahangarsu a kan irin wadannan batutuwa.

Haka nan kuma wani abu da taron zai dubi a kansa shi ne yadda aka samu kalmomi da suk edaidai da juna a cikin dukkanin littafan, da suka hada da sunayen wasu wurare, da kuma sunayen surori.

3614932


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna morocco
captcha