IQNA

An Girmama Wadanda Suka Kwazo A Gasar Kur’ani A Yemen

23:54 - July 06, 2017
Lambar Labari: 3481674
Bangaren kasa da kasa,an nuna wadanda suka nuna kwazoa gasar karatun kur’ani mai tsarki da akagudanar a gundumar Ibb a kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna nya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Akhbar News cewa, wafa Al’ashari babbar daraktabn cibiyar kula da ayyukan alhari ta gungumar Ibb ta bayyana cewa, wannan gasa dai ta kunshi mata zalla.

Ta kara da cewa an kawo karshen gasar cikin nasara tare da halartar mata daga sassa na wannan gunduma, dsa suka hada da makaranta da kuma mahardata, inda aka gudanar da gasar tare da yin alkalanci na mata zalla.

Ta kara da cewa babar manufar wannan gasa dai iota ce kara karfafa mata akan lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki, duk kuwa da irin matsalolin da kasa take ciki nay akin da aka kallafa mata, amma dai matan sun nuna jajircewa wajen ganin ba abar su a baya wajen sha’anin kur’ani.

Daga karshe ta bayyana cewa an bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka halrci gasar, kamar yadda kuma aka bayar da wasu kyautukan ga wadanda suka fi nuna kwazo.

3615973


captcha