Sheikh Bashir Ahmed Siddiq, Shehin Malaman Masallacin Annabi ya rasu a yau Alhamis yana da shekaru 90 a duniya.
An haifi Sheikh Bashir a kasar Indiya, kuma ya koma Madina tun yana karami, inda ya dukufa wajen karantar da kur’ani mai tsarki da karanta shi a masallacin Annabi.
Wasu fitattun mahardatan kur’ani da suka hada da Sheikh Muhammad Ayyub da Sheikh Ali Jaber wadanda suka yi limamai a masallacin Annabi da kuma babban masallacin Harami da ke Makkah, sun kammala karatunsu a karkashin kulawar sa.
Sheikh Bashir ya shahara wajen koyar da hadisai da tsantsar riko da ingantattun takardu, wanda hakan ya sanya shi amintacce a kan ilimin karatun kur’ani.
A yau ne aka sanar da rasuwar Sheikh kuma aka yi masa addu’a bayan an idar da sallar asuba a masallacin Annabi. Daruruwan malamai da dalibai ne suka halarci jana'izar sa.