Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren huldda da jama’a na ciyar yad aal’and muslunci cewa, wannan shiri ya gudana cikin nasara, inda aka bayar da horo ga malaman kur’ani da za su iya bayar da gudunmawa wajen koyar da daliban kur’ani makarantu da cibiyoyin muslnci a kasar.
Ali Bakhtiyari shi ne shugaban ofishin yada al’adun muslunci na Iran a Uganda, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa ya bayyana cewa, wannan shiri yana daga cikin muhimman abubuwan da Iran ta mayar da hankali a kansu a halin yanzu, bisa umarnin jagoran juyin juya halin muslunci.
Ya ci gaba da cewa wannan shiri zai bayar da damar kara bunkasa ayyuka a fagen kur’ani, da hakan ya hada da sanin ka’idojin karatunsa da kuma hardarsa, gami da ilmomin da suke kunshe a cikin wannan littafi mai tsarki.
Daga karshe an gudanar da jarabawa ga wadanda suka halarci horon kuma an bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.
An gudanare da shirin ne tare da hadin gwiwa da karamin ofishin jakadancin Iran da kuma bangaren kur’ani na kwalejin Almustafa da ke Uganda.