Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, A cikin jawabin da ya gabatar a daren jiya wanda tashoshin talabijin suka watsa kai tsaye, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, manyan malaman addini musamman babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun nasara a yaki kan ISIS a kasar, domin kuwa shi ne ya bayar da fatawa wadda al'ummar Iraki suka yi amfani da ita wajen fatattakar 'yan ta'adda.
Kamar yadda ya jinjina wa kasar Iran kan irin gudunmawar da ta bai wa Irakia dukkanin bangarori har Iraki ta kai ga samun wannan gagarumar nasara, musamman Ayatollah sayyid Ali Khameni jagoran juyin Isalama na kasar.
Haka nan kuma ya bayyana wannan nasara da cewa za ta yi gagarumin tasisri wajen karya lagon 'yan ta'addan ISIS da kuma masu daukar nauyinsu daga cikin kasashen yankin.