Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar yaum Sabi cewa, Sayyid Mus'ad bababn daraktan ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar reshen Alkahira ya bayyana cewa, koyar da yara hardar kur'ani na kare su daga karkata ga munanan ayyuka da suka hada da ta'addanci.
Ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban wani taro da aka shirya kan hardar kur'ani mai tsarki a birnin Alkahira a karkashin ma'aikatarsa.
Ya ce ko shakka babu hardar kur'ani mai tsarki tana da bababn tasiri a cikin lamarin musulmi ta fukskar tarbiya, musamman ma dai ga kananan yara maso tasuwa, ta yadda idan tunaninsu ya ginu a kan kur'ani, zai basu damar shagaltuwa da sha'anin kurani kadai a rayuwarsu.
Haka nan kuma ya yi ishara da matsalar ta'addanci da sunan addini ko sunna, inda ya ce rashin fahimtar addini ne ya jawo hakan, kuma idan aka koyar da yara kur'ani hakikanin ma'anoninsa suka rike, to zai taimaka msuu wajen tashi da sahihin tunani.
3618163