Haisam Anwar mai kula da harkokin al'adu na wannan cibiya ta darul kutub ya bayyana cewa, lojaci yana da matukar muhimamnci a mahangar addinin kur'ani muslunci kamar yadda kur'ani ya nuna haka a bayyane.
Ya ce a cikin kur'ani akwai sura mai suna asr, wato lokaci, kuma surar ta fara ne da rantsuwa da Allah madaukakin sarki ya yi da lokaci, wanda hakan ke nuni da cewa hakika lokaci abu ne mai matukar muhimamnci da matsayi na musamman a cikin wannan addini.
Baya ga haka kuma dukkanin ayyukan ibada da ke cikin shikashikan muslunci kama daga salla, azumi, hajji duk sun doru ne a kan wasu lokuta na musamman domin aiwatar da su.
Kamar yadda a cikin surat Yusuf (AS) aka yi magana akan batun lokaci na noma da kuma fari, ta yadda aka bayar da bayanin shekaru da za ayi noma da kuma tanadin abinci a cikin wadannan shekaru, da kuma yin tsimi dmoin shekarun fari, da sauran abubuwa da dama da suka danganci lokaci da kur'ani mai tsarki ya yi ishara da su.