IQNA

An Kur'anin Da Aka Yi Wa Gyara Tsawon Shekaru 6 A Masar

20:24 - July 18, 2017
Lambar Labari: 3481711
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka yi wa gyara har tsawon shekaru 6ba jere da aka danganta shi da lokacin khalifa Usman.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alhayat cewa, an kafa kwamiti na mutane bakwai kwararru kan gyara kayan tarihi.

Bayanin ya ce baan kwashe tsawons hekaru shida a jere suna yin aiki, daga karshe sun samu nasaar gyara wannan kur'ani ta yadda suka mika shi a kwafin kur'ani guda daya.

Tun a cikin shekara ta 1870 cibiyar darul kur'an ta Masar ta samu wanann kur'ani, wanda ake danganta zuwansa Masar a lokacin Amru bin As, wato a cikin karni na farko na hijira kamariya, bayan daukar tsawon lokaci yana ajiye, wasu bangarorinsa sun fara lalacewa, wanda ahakn ya sanya aka kafa kwamitin gyaransa tun shekaru 6 da suka gabata, bayan kammala aikin a wannan makon an nuna shi a cikin cibiyar Darul kur'an da ke Alkhira.

Daruruwan Misrawa ne dai suke da isa wurin domin duba wanann kwafin kur'ani mai tsarki, duk kuwa da cewa akwai matakan tsaro domin tabbatar da cewa an ci gaba da adana shi a cikin aminci.

Sakamakon wani bincike da masu gano kayan tarihi suka yi da suka hada har da 'yan kasar Birtaniya a kan wannan kur'ani, sun iya gano cewa tarihin wannan kur'ani yana komawa ne zuwa ga shekru kusan dubu daya da dari hudu.

3620211


captcha