Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, tashar talabijin ta al'alam ta bayar da rahoton cewa, a zaman da kotun
sojin ta gudanar ta bayyana cewa, dukkanin mutanen 58 suna da hannu a harin da
aka kaddamar kan ofishin 'yan sanda da ke garin Asyut, a lokacin da ake gudanar
da zanga-zangar da ta kai ga hambarar da Muhammad Morsi daga kan shugabancin
kasar a 2013.
Kotun ta ce dukkanin mutanen 58 da ake tuhuma mambobi ne na kungiyar muslim Brotherhood, kuma ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kansu.
Shugaban kasar mai ci a yanzu Abdulfattah Sisi ya yi amfani da damar da ya samu a lokacin da mutane suke yin zanga-zangar nuna adawa ga Muhammad Morsi, inda kasashen Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa suka taimaka masa wajen hambarar da shi, inda ya dare kan shugabancin kasar har zuwa yanzu.