IQNA

Kwamitin Shari’a Ya Aince Da Tsarin Bankin Musulunci A Morocco

23:33 - July 29, 2017
Lambar Labari: 3481747
Bangaren kasa da kasa, kwamitin shari’a na kasar Morocco ya amince da tsarin bankin musulunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na MEMO ya habarta cewa, kwamitin shari’a na kasar ya amince da bukatar da aka gabatar masa tun lokutan baya domin fara yina iki da tsarin bankin musulunci a kasar.

Talal Lahlu jami’I ne a babban bankin kasar ta Morocco ya bayyana cewa, babban bankin kasar ne ya mika wanann bukata ga kwamitin shari’a na kasar, domin fara amfani tsarin bankin muslunci a kasar, wanda ga dukkanin alamu zai samu karbuwa a kasar.

Bankin musulunci ya kafa rassansa a cikin biranan Ribat da kuma Kazablanka, amma bai fara gudanar da ayyukansa ba, saboda rashin samun izini daga kwamitin shari’a na kasar.

Kasar Moroco na daga cikin kasashen larabawan arewacin Afirka da ke samun masu yawon shakatawa daga kasashen duniya, da hakan ya hada har daga kasashen msuulmi, inda bankin ke ganin wannan babbar dama ce ta samun masu saka hannayen jari.

3624184


captcha