IQNA

Bude Masallaci Mafi Jimawa A kasar Girka

21:55 - August 17, 2017
Lambar Labari: 3481806
Bangaren kasa da kasa, an bude masallaci mafi jimawa a kasar Girka a yankin Agurai da ke gefen birnin Athen fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na greekreporter cewa, ministan yada al'adu na kasar ne ya sanar da hakan, inda ya ce wannan masallaci zai ci gaba da zama wurin tarihi da suke alfahari da shi.

An gina wannan masallacin nea cikin shekara ta 1456 bayan rusa majami'oin basilica da mayakan dauar Usmaniya suka yia cikin Girka.

A cikin tsawon shekaru yaki da mayakan daular Usamniyya da kuma al'ummar Girka, an sake mayar da shi zuwa majami'a, amma a cikin shekara ta 1824, an mayar da wannan masallaci makaranta, bayan samun 'yancin kai a Girka, an mayar da wannan masallacia matsayin gidan kaso na sojoji, daga bisani kuma ya koma gidan biredi na sojoji.

A farkon karni na ashirin, an mayar da wannan masallaci wurin bincike na ilimi da kuma adana wasu daga cikin kayan tarihin kasar, a shekara ta 2010, an bayar da aikin gyaransa wanda aka kammala a halin yanzu, kuma ministan raya al'adu na kasar zai jagoranci bude shi.

3631585

captcha