Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, majalisar dokokin kasar Sweden ta sanar da nan ba da jimawa ba za ta gudanar da zama na musamman, domin kada kuri’a kan daftarin kudirin da ke nemna a hana shigo da naman halal na musulmi da kuma yankan yahudawa a cikin kasar.
Tun kimanin watanni biyu da suka gabata ne wasu ‘yan majalisar dokokin kasar suka gabatar da wannan kudiri, wanda za a kada kuri’a a nasa, amma dai majalisar ba ta ayyana ranar gudanar da kada kuri’a a kan wannan daftarin kudiri ba.
Harburt Wniter shi ne shugaban babbar kungiyar yahudawa a kasar ta Sweden, ya bayyana cewa idan majalisar dokokin kasar ta amince da wannan daftari, to za atauye musu wani bangare na hakkokinsu na addini.
Adadin mutane kasar Sweden dai ya kai kimanin miliyan 8, 17,500 yahudawa ne, yayin da adadin musulmin kasar ya kai dubu 450 na dukkanin al’ummar kasar baki daya.