Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Al-nahar da kasar Lebanon cewa, majiyar hukumar shige da fishe na kasar Saudia tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa mahajjata 1,313,946 suka isa kasar ta tashar jiragen sama, sannan wasu 79,501 ta kasa, a yayinda wasu 12,477 suka isa kasar ta Ruwa.
Hukumar ta kara da cewa tana saran kafin a rufe tashoshin jiragen sama da jiragen ruwa sa kuma bodojin kasar yawan mahajjatan bana zai kai miliyon biyu.
Majiyar ta kara da cewa, a bana yawan mahajjata ya karu da kashi talatin da uku idan an twatanta da shekaran da ta gabata.
Mahajjana kasar Iran fiye da dubu tamanin suka isa kasar saudia ya zuwa yanzu. Iraniyawa basu sami damar zuwa hajji a shekarara da ta gabata ba, don rashin amincewar da gwamnatin kasar Iran tayi kan sharuddan da gwamnatin saudia ta shimfina masu.