Emilian dan shekaru 29 da haihuwa a duniya , yana daga cikin mutaen da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya amince da su matuka, kuma yake saurarensa a kan batutuwa da suka shafi siyasa.
Tun kafin zaben Emanuel Macron, Isma'il Emilian ya kasance shi ne shugaban yakin neman zaben Macron, kuma ya taka gagarumar rawa wajen shimfida hanyar nasarar Macrona lokacin zaben shugaban kasar Faransa.
Yanzu haka dai yana a matsayin babban mai bayar da shawara kuma na hannun dammar shugaban kasar Faransa Emanuel;l macron, wanda shi ma matashi dan shekaru talatin da 'yan kai.