Wannan lamari ya bakanta ran wasu daga cikin masana kan harkokin ilimi da suke bin diddigi lamurra a cikin kasashen nahiyar turai, inda suke kallon cewa bullar irin wannan matsala ya sanya ana ganin akwai yiwuwar a samu matsala.
Kasar Denmark ta fara fuskantar bullar wasu kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin kymaar addinin muslunci da kuma baki masu zuwa kasar, wanda hakan yake nuna yadda ake samun karuwar masu gaba da addini a cikin kasashen turaia wannan lokaci.
Guguwar kyamar msulunci ta fara kadawa ne tun kimanin shekaru biyar da suka gabata acikin kasashen turai, amma lamarin ya kara tsananta ne bayan da shugaban amurka mai ci yanzu ya dare kan kujerar mulki.
Babbar barazanar kyamar muslunci dai tana a matsayin wani abu mai matukar tayar da hankali da kuma mayar da hannun agogo baya azamantakewar al'ummomi a nahiyar.