Ya ce abbu zatoi babu tsammani ya kamu da wata rashin lafiya mai ban mamaki, wanda kuma abin da yafi ban mamaki a cikin lamarin shi ne, yadda likita ya ce karatun kur'ani ne kawai maganain rashin lafiyar.
Haji Abdullah ya ci gaba da cewa ya kasance a lokacin baya iya karatu ko rubtu, amma da yake likita ya lizimta masa yin haka, ya zama wajibi a kansa ya nemi yadda zai koyi karatun kur'ani mai tsarki.
A matakin farko dai ya fara saurare ne daga masu karatu, a lokaci guda kuma shi ma yana koyo kuma yana rubutawa, sannu a hankali har ya rubuta kur'ani mai tsarki baki daya.
Ya ci gaba da cewa bai fuskanci wata wahala ba a cikin rubutun kur'ani, kuma zai ci gaba da yi, domin ta hakan ne kur'ani zai zauna a cikin kwalwarsa.