Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da
rahoton cewa, wata kungiya ta mabiya amzhabar iyalan gidan manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a birnin
Toronto na kasar Canada za ta gudanar da bababn taron Ashura a wannan shekara.
Bayanin ya ce taron zai fara ne daga kimanin 11 na ranar Ashura a birnin Toronto, inda za a fara haduwa a wannan ban fili da ke cikin birnin, daga nan kuma za a zagaya a kan titunan babbar jami'ar Toronto.
Bayan kammala zagayen za a gabatar da jawabai a kan matsayin Imam Hussain (AS) da kuma darussan da suke kunshe a cikin rayuwarsa da kuma sadaukarwar da ya yi domin wanzuwar addinin manzon Allah bisa koyarsa.
An fara gudanar da wannan taron ne tun kimanin shekaru biyu da suka gabata, inda a shekarar da ta gabata fiye da mutane dubu uku da dari biyar ne suka shiga cikin taron.