IQNA

21:10 - September 29, 2017
Lambar Labari: 3481947
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar Iraki ta sanar da cewa jami’an tsaro sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai harin kunar bakin wake a yankin Kazimain.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa shafin yada labarai na shafaqana ya bayar da rahoton cewa, a yau ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar Iraki ta sanar da cewa jami’an tsaron kasar sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai harin kunar bakin wake a yankin Kazimain da aka shirya kaiwa aranar gomaga watana muharram.

Wahhab Ta’i shi ne babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaroa ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Iraki ya bayyana cewa, jami’an tsaron sun samu wasu bayanan sirri ne da suka ba su damar gano wanann shiri, wanda yan ta’adda suka shirya daga yankin Karama da ke cikin Bagdad.

Bisa ga abin da ‘yan ta’adda suka shuka shirya da, ranar goma ga watan muharram za su kai wasu munanan hare-harea lokacin da mabiya mazhaba iyalan gidan manzon Allah ke juyayin ashura a yankin na Kazimain.

Jami’an tsaro sun sau nasarar halaka ‘yan ta’adan baki daya da suke da wannan mummunan shiri.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki dai ta dauki dukkanin matakai domin ganin an tabbatar da tsaro da kuma kare rayukan fararen hula a lokutan gudanar da tarukan ashura.

3647744


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ashura ، Iraki ، Kazimain ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: