Masu makokin dai suna dauke ne da tutoci da kuma kwafin kur'anai a hannuwasu da suke dagawa sama, a matsayin alama ta juyiyin Ashura da kuma nuna matsayin tawagarsu ta mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki, domin kara daukaka matsayin kur'ani a cikin wannan taro mai albarka.
Wannan dai ba shi ne karon farko da makarantar kur'ani da mahardata suke shiga cikin tawagogi domin gudanar da tarukan tunawa da zagayowar Ashura ba.
Koa shekarun baya an gudanar kamar haka, inda tagawar takan kunshi malamai masu koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki, da kuma dalibai da suka hada da makaranta da kuma mahardata.