IQNA

Miliyoyin Mutane Sun Halarci Taron Makoki A Karbala

23:42 - October 01, 2017
Lambar Labari: 3481956
Bangaren kasa da kasa, Mahukuntan Iraki sun bayyana cewa yawan jama'ar da ke halartar zaman makokin ranar Ashura a birnin Karbala na kasar sun haura mutane miliyan shida daga ciki da wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, Mahukuntan Iraki sun bayyana cewa, Ana ci gaba da samun tururruwan jama'a da suke zuwa birnin Karbala domin gudanar da juyayin ranar Ashura a ranar goma ga watan Muharram lamarin da ke nuni da cewa mutanen da suke halartar taron ya wuce duk yadda aka yi zato.

Shugaban bangaren sanarwa a cibiyar kula da masu ziyarar wajaje masu tsarki a kasar Iraki a jiya Asabar ya bayyana cewa, a halin yanzu haka birnin Karbala yana ci gaba da karbar baki daga ciki da wajen kasar da suka zo domin gudanar da juyayin ranar Ashura a ranar 10 ga watan Muharram, don haka ake hasashen yawan jama'ar da zasu halacci juyayin na bana zai haura mutane miliyan shida inda ko a shekararda ta gabata fiye da mutane miliyan biyu ne suka gudanar da juyayin.

A yau Lahadi ne dai ake gudanar da zaman taron juyayin Ashura a birnin Karbala na kasar Iraki domin jaddada alhini da juyayi kan gisan gillar da Bani-Umayyah da magoya bayansu suka yi wa jikan manzon Allah kuma daya daga cikin shugabannin samarin gidan aljanna Imam Husani dan Ali dan Abi-Talib amincin Allah ya tabbat a gare shi da iyalan gidansa da sahabbansa da ba su wuce saba’in da biyu ba, a filin Karbala na kasar Iraki a shekara ta 61 bayan hijira, bayan sun bijirewa mulkin kama karya da bakin zalunci na mahukuntan Bani-Umayyah karkashin ja'irin shugaba Yazid dan Mu'awiya da dukkanin Musulmi suka yi tarayya kan fasikancinsa da rashin cancantarsa ga jagorancin al'ummar musulmi.

3647946


captcha