Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na silive cewa, an gudanar da zaman ne wajen wani
cin abincin dare da aka shirya, tare da halartar malamai daga bangaren addinin
muslunci da kuma shugabannin majami'ar.
Brayen Mike Winey shi ne babban malami na cocin katolika ta birnin New York ya bayyana a wajen taron cewa, tun kimanin shekaru 15 da suka gabata ne suka fara gudanar da irin wannan zama tare da 'yan uwansu musulmi da nufi kara karfafa alaka da fahimtar juna.
Na'in Bik shi ne babban daraktan cibiyar bunkasa harkokin muslunci a arewacin Amurka ya bayyana a wajen taron cewa, hakika irin wannan haduwa tana da matukar muhimmanci, domin kuwa tana kara tabbatar da wajabcin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin kiristanci da muslunci wadanda 'yan uwan juna.