IQNA

Amurka Da Isra'ila Na Da Hannu A Murabus Din Hariri

21:22 - November 05, 2017
Lambar Labari: 3482069
Bangaren kasa da kasa, Ibrahim Karagol fitaccen dan jarida na kasa da kasa, ya bayyana murabus din da Hariri ya yi a matsayin aikin Amurka da Isr'aila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ibrahim Karagol bababn editan jaridar Yeni shafaq fitaccen dan jarida na kasa da kasa, ya bayyana murabus din da Hariri ya yi a matsayin aikin Amurka da Isr'aila da kuma 'yan korensu daga cikin sarakunan larabawa.

A nasu bangaren Jami'an tsaron kasar Lebanon sun karyata ikirarin da firayi ministan kasar mai murabus Saad Hariri ya yi, kan cewa ana yin barazana ga rayuwarsa.

A jiya Asabar ne dai Hariri ya yi murabus ba zato ba tsammani daga birnin Riyad na Saudiyya, bayan da masarautar Saudiyya ta kiraye shi a ranar Juma'ar da ta gabata.

Hariri ya ce ya yi murabus ne saboda Iran tana tsoma baki a cikin harkokin Lebanon, kuma ana yin barazana ga rayuwarsa. Bayyana hakan ke da wuya sai gwamnatocin Amurka, Saudiyya da Isra'ila suka yi na'am da matakin nasa, tare da yin kira da a dauki mataki na fuskantar Iran.

Sai dai Iran da ma wasu masana da dama suna ganin cewa wadannan gwamnatocin uku su ne suka shirya hakan, tare da tilasta Hariri yin murabus, da nufin yin amfani da hakan wajen sake dagula lamurra a Lebanon, bayan da suka sha kashi a Syria da Iraki.

Saad Hariri dai yana daga cikin mutane masu alaka da Sarakunan Al saud, inda yakan samu kwangila ta biliyoyin daloli daga gare su, wanda hakan yasa bashi da ikon tayar da maganar da suka yi masa ko saba umarnin da suka bashi.

3660142


captcha