Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al'adun musulunci cewa, a jiya an
bude wani baje koli a birnin Dakar na kasar Senegal na littafai da aka rubuta
kan manyan malaman Iran da Senegal da suka hada da Imam Khomenei (RA) da kuam
Sheikh Amadu Bamba jagoran darikar Muridiyya a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gabatar da littafai kimanin 67 da aka rubuta acikin harsunan faransanci da kuma larabaci da aka rubuta a Iran da Senegal.
Babbar manufar wanann baje koli dai ita ce bayyana matsayin dukkanin bangarorin biyu na malaman Iran da kuma na Senegal, wadanda dukkaninsu sun hadua kan abubuwa da dama, musamman soyayya ga ahlul bait.
Za a kammala wannan baje koli ne gobe, tare da gabatar da jawabai ga maharta wurin, inda za a bayyana mahangar malaman biyu Imam Khomeni (RA) da kuam sheikh Amadu Bamba a kan lamurra da suka shafi tafsirin wasu surori na kur'ani.