IQNA

Gudunmaar Hubbaren Alawi A Tarukan Tunawa Da Shahadar Imam Askari (As)

23:31 - November 27, 2017
Lambar Labari: 3482143
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Hassan (AS) hubbaren Imam Ali (AS ya bayar da gudunamawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin hulda da jama’a na hubbaren Alawi ya habarta cewa, shikh Sattar Murshidi shugaban kula da ayyukan hubbaren Imamai biyu mas tsarki a Saira ya bayyana cewa, a yayin tarukan tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Hassan (AS) hubbaren Imam Ali (AS) ya bayar da gudunamawa a dukkanin bangarori.

Ya ci gaba da cewa daga cikin irin taimakon da aka samu baya ga na kudade da kuma kuma kayan aiki na tarbar jama’a, an samu taimako a bangarorin wakafi.

Sayyid rahman Fayyad shi ne shugaban bangaren kula da hulda da jama’a na hubarorin Askariyain amincin Allah ya tabbata a gare shu, ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a dukkanin bangarori a wannan karo a yayin shirin gudanar da tarukan.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, awai tawagogi 250 gami da dubban mutane da suka taimaka wajen tabbar da tsari, da hakan ya hada har da bangaren tsaro.

3667458


captcha