Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa,a shirye-shiryen gudanar da taron makon hadin kai, wata bababr tawaga daga kasar Senegal za ta halrci taron, daga cikin akwai Muhamamd Lamin Lai kakakin darikar lai, sai kuma sheikh Abdulmun'im Zaid shugaban mabiya tafarkin ahlul bait (AS) a kasar.
Sheikhuna Lu shi ne wakilin darikar Muridiyyah kuma wanda ya tarjama kur'ani kur'ani mai tsarkia cikin harshen Wolof, yana daga cikin wannan tawaga daga kasar Senegal.
Taron makon hadin kai karo na 31 zai gudana ne a ehran kamar yadda aka saba tare da halartar malamai da masana daga kasashen duniya.