Kamfanin dillancin labaran iqna
ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar yanar gizo ta yaum sabi cewa, an bude
wannan taron jiya a a bababn dakin taruka na birnin Akahira tare da halatar
shugaban kasar Masar Abdulfattaha Sisi.
Baya ga shugaban na Masar Ahmad Tayyib shugaban cibiyar Azahar, Muhamma Mukhtar ministan kula da harkokin addini na kasar Masar, Shauki Allam bababn maia bayar da fatawa a kasar, duk sun halarci wurin.
Haka nan kuma wasu daga cikin manyan fitattun malaman kasar da suka hada da limaman juma’a na wasu manyan masallatai a branan kasar duk sun halarci wurin.
A karshen zaman taron na jiya bayan sauraren karatun kur’ani da kuma bayanai kan matsayin da daraja da wadannan ranaku na tunawa da haihuwar manzon Allah suke ad shi da muhimmancin raya su, an girmama Muhamamd Bushara, shugaban kwamitin ayyuka na musulmia nahiyar turai, uma shugaban kwamitin muuslmin kasar Faransa, kuma shugaban cibiyar ilimi ta bn Sina.