IQNA

23:32 - December 16, 2017
Lambar Labari: 3482206
Bangaren kasa da kasa, malaman addinin muslunci a kasar Senegal sun yi Allawadai da kudirin Trump a kan masallacin quds.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, a wani zaman taro da aka gudanar jiya a fadar mulkin kasar Senegal Dakar malaman addinin muslunci na kasar sun yi Allawadai da kudirin Trump a kan masallacin quds mai afarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zama an gudanar da shi ne musamman domin yin bahasi kan irin matakin cin zarafi da wulakanci ga muuslmi da rump ya dauka na amincewa da birnin Quds a matsayin fadar mulkin yahudawan sahyuniya.

Irin wannan mataki dai na fuskantar kalu balae daga koina cikin fadin duniya daga bangaren musulmi da ma wadanda a musulmi da ma wadanda ba musulmi, da kawayn Amurka daga cikin kasashen yammacin turai da kuma wasu ‘yan korenta.

Daga cikin malaman da suka gabatar da jawabia  wajen wannan taro akwai malaman darikun sufaye daban-daban wadanda su ne suke da babban tasiri ta fuskar addinin musluni akasar.

Haka nan kuma an sau halartar wasu daga cikin bai ‘yan kasashen ketare da suka hada har da jami’an huldar diflomasiyya na wasu kasashen msuulmia  cikin kasar ta Senegal da suka gabatar da bayanai.

Daga karshe taro ya jadda goyon bayansa ga sakamakon taron da aka gudanar na kasashen msuulmi na kin aminewa da wannan kudiri na Trump, tare da jadda amiewa da birnin Quds a matsayin fadar mulkin palastine.

3672994

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: