IQNA

23:50 - December 29, 2017
Lambar Labari: 3482250
Bangaren kasa da kasa, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin Kabul na Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Quds Al-arabi cewa, a cikin bayanin da ya fitar kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin Kabul na Afghanistan wanda ya yi sanaiyyar mutuwa tare da jikkatar mutane fiye da 120.

Bayanin kwamitin tsaron ya ce irin wadannan ayyukan ta’addanci babu wani abu da zai iya zama hujja ta aikata su, face rashin imani da rashin ‘yan adamtaka a cikin zukatan masu aikata haka.

Haka nan kuma bayanin ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukasu, da kuma yin fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka sakamakon wannan harin ta’addanci.

Kwamitin tsaro ya kirayi dukkanin bangarori na kasa da kasa da su yi aiki tae da gwamnatin Afghanistan domin fuskatantar wannan babban kalu bale na tsaro da ke a gabanta.

A jiya ne aka kai harin ta’addanci a kan wata cibiyar yada al’adu da ke cikin birnin Kabul, inda aka kasha mutane 40 wasu fiye da 80 kuma suka samu raunuka, kungiyar ‘yan ta’addan wahabiyawa ta Daesh ta dauki alhain kai harin.

3677310

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: