IQNA

'Yan Boko Haram Sun Kashe Fararen Hula

16:30 - December 31, 2017
Lambar Labari: 3482254
Bangaren kasa da kasa, 'yan ta'addan Boko haram sun kashe wasu fararen hula masu aikin katako a kusa da birnin Maiduguri.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan ta'addan kungiyar Boko haram sun kashe wasu masu sana'ar katako su hudu a wani wuri mai nisan kilo mita 20 daga birnin Maiduguri na jahar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Nigeriya.

Tashar Sky News ta watsa rahoton cewa, 'yan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a kan wasu manyan motoci guda uku da suke dauke da katako da ke kan hanyar isa zuwa cikin birnin Maiduguri.

Haruna Dahiru daya ne daga cikin wadanda suka tsira daga harin, ya kuma bayyana cewa; su 16 suke tafe da katakon, kuma 'yan ta'addan sun yi musu kwantan bauna ne, inda suka bude musu wuta, ya ce a nan take dai sun kashe hudu daga cikin abokan aikinsa.

Kididdigar majalisar dinkin duniya ta yi nuni da cewa kimanin mutane 20,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da miliya 2.6 suka gudu suka bar muhallansu, inda a halin yanzu suke tsugunne a sansanonin 'yan gudun hijira, ko kuma suke watangaririya  a wasu biranan arewacin Najeriya da kuma kasashe makwafta.

3677912

 

 

 

 

 

captcha