IQNA

Kyautar Kwafin Kur’ani Dubu 15 Ga Matasa A Jibouti

23:39 - January 03, 2018
Lambar Labari: 3482263
Bangaren kasa da kasa, kungiyar matasa musulmi ta duniya ta bayar da kyautar kwafin kur’ani guda dubu 15 ga matasan kasar Jbouti.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na watny1.com cewa, a jiya kungiyar matasa musulmi ta duniya ta bayar da kyautar kwafin kur’ani guda dubu 15 ga matasan kasar Jbouti tare da halartar jami’ai daga ma’atun ilimi da yada al’adu na kasar.

Babban daraktan harkokin ilimi na kasar shi ne ya karbi wadannan kwafin kur’ani daga wakilan kungiyar ta matasa, inda aka mika su ga wasu makarantu na adini da kekasar.

A taron karbar wannan kyautuka an gayyaci shugabannin makarantun da za su samu tallafin wadannan kwafin kur’anai domin karabr abin da makarantun nasu suka samu.

Daraktan ya bayyana cewa, hakika irin wannan kokari da kungiyar matasa musulmi take yi babban abin yabo ne, kuma yana fatan wannan aiki da aka yi domin Allah ya zama karbabbe kuma ya bayar da lada ga dukkanin wadanada suke da hannu a cikin lamarin.

3678899

 

 

 

 

captcha