Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar almisriyun cewa, a jiya ne aka bude babban taron gidajen radiyon kr’ani na kasa da kasa karo na hudu a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar mai taken fada da satsauran ra’ayi da addinin muslunci.
Babban daraktan hadin gwiwar tashoshin radiyo na kur’ani na duniya ya bayyana a wajen bude taron cewa, babbar manufarsu ta zabar wannan take ga wannan taro ita ce, duba irin gudunmawar da kafofin sadrawa na kur’ani suke bayarwa wajen danwafe kurbatattun akidu da suke bata sunan muslunci.
Ya ce akwai masu yin afani da sunan muslunci da ma kur’ani wajen bata sunan addini, inda suke yin aiki da duk abin da suka karanta ba tare da sun fahimci ma’anarsa ko tawilinsa ba, inda suka mayar da tsatsauran ra’ayi da ta’adanci a matsayin koyarwar kur’ani.
Muhammad Mukhtar Juma’a, ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ya bayyana a wurin taron cewa, kafofin yada labarai na muslunci suna gagarumar gudunmawa da za su bayar wajen wayar da muuslmi musamman matasa da ake rudarsu suna karbar akidun ta’addanci da sunan addini.
Zainab Wakil, mataimakiyar babban daraktan ma’aikatar kula ilimi ta kasar Masar ta bayyana cewa, suna araba da duk wani mataki da kafofin ada labarai za su dauka na wayar da kan jama’a kan hakikanin koyarwar muslunci.
Taron yana samun halartar wakilai daga kasashe daban-daban, da suka hada da Kuwait, Oman, UAE, Mauritania, Malaysia, Saudia, Senegal, Bahrain, Jordan da kuma Aljeriya.