IQNA

Tarjamar Hikomomin Nahjul Balagha A Senegal

23:49 - February 03, 2018
Lambar Labari: 3482360
Bangaren kasa da kasa, an rattaba hannu kan wata wata yarjejeniya ta gudanar da aiki tare wajen tarjama hikimomin littafin nahjul Balagha da ma wasu litafan malaman kasar Iran a Senegal.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka rattaba hannu kan wata wata yarjejeniya ta gudanar da aiki tare tsakanin karamin ofishin jakadancin Iran da kuma cibiyar buga littafai na darikar Muridiyya wajen tarjama hikimomin littafin nahjul Balagha da ma wasu litafan malaman kasar Iran a Senegal a cikin harsunan da mutanen kasar ke magana da su.

Mustafa Anja shi ne babban daraktan cibiyar buga littafai ta mabiya darikar sufaye da muridiyya a kasar Senegal, ya bayyana cewa za su yi aiki tare da bangaren domin ganin an tarjama littafai na addinin muslunci.

Ya kara da cewa, Iran tana da matukar muhimmanci a duniyar musulunci, domin kuwa mafi yawa malaman da suka suka yi rubut a ciki adini a tarihi Ianiyawa, kama daga manyan malaman sunna da kuma shi’a, da hakan ya hada da Buhari da muslim da kuma ibn majah da auransu, kamar yadda babban malamin sunna maubucin tafsiri wato fakhruddin razi da ibn sina da Abu Raihan da sauransu duk Iraniyawa ne, kamar yadda a bangaren malaman mazhabar shi’ar ahlul bait dama ba a magana.

Ya ce aikin da za su mayar da hankali kansu yanzu shi ne tarjama kalamai da hudubobin nahjul balagha na Imam Ali (AS) zuwa harsunan da ake yin magana da su a kasar Senegal, domin afanin alumma.

3687859

 

captcha