IQNA

Nuna Goyon Baya Ga Palastinu Na Daga Cikin Siyasar India

23:48 - February 11, 2018
Lambar Labari: 3482387
Bangaren kasa da kasa, Narendra Modi firayi ministan Indiya a wani ran gadi da ya kaddamar da yankin gabas ta tsakiya, ya ziyarci yankunan Palastinawa, wacce ita ce irinta ta farko ta wani shugaban gwamnatin Indiya a wannan yankin.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ziyarar ta Modi ta zo 'yan makwanni kadan bayan ganawarsa da firayi ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin New Delhi.

A yayin ziyarar tasa, Mista Modi, ya gana da shugaban Palastinawa Mahmud Abass, wanda ya bayyana ziyarar mai cike da tarihi.

Mahmud Abass ya fada a yayin ganawar cewa '' Palastinu har ko da yaushe tana maraba da hawa kan teburin tattaunawa ta zaman lafiya, amma ta hanyar shirya muhawara ta kasa da kasa da girka wani shiri mai nagarta don shiga tsakanin tattaunawar, don haka ''

A nasa bangare kuwa firayi ministan Indiya, ya ce yana fatan ganin Palastinu ta samu yancinta nan bada jimawa ba.

Indiya dai na daga cikin kasashen da suka jiyawa matakin Amurka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin yahudawan mamaya na Isra'la baya.

3690441

 

 

 

captcha