IQNA

Ra’ayoyi Mabanbanta Dangane Da Furucin Dan Wasan Kwaikwayo Na Saudiyya

23:27 - February 25, 2018
Lambar Labari: 3482429
Bangaren kasa da kasa, dangane da wani furuci da Nasir Qasabi dan wasan kwaikwayo na Saudiyya yay i kan shafinsa na twitter kan muhimmancin karatun kur’ani an samu ra’ayoyi mambanta.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alyaum24.com cewa, Nasir Qasabi dan wasan kwaikwayo na Saudiyya  dangane da wani furuci da ya yi kan shafinsa na twitter kan uhimmancin karatun kur’ani an samu ra’ayoyi mambantaa tsakanin masu binsa shafinsa.

A cikin shafin nasa ya rubuta cewa; karatun kur’ani mai tsarki yana bude muryar mutum ta yi kyau sosai, sannan kuma yana kara ma mutum fasahar magana.

Wannan furuci ya fusata wasu, inda suke ganin cewa danganta kur’ani da batun kyawun sauti musamman gare su ‘yan wasan kwaikwayo, hakan cin zarafin kur’ani ne, yayin da kuma wasu suke ganin hakan a matsayin magana mai kyau.

Ya ce tun suna dalibai a jami’a wani malaminsu yana gaya musu cewa, su rika karanta kur’ani za su samu fasahar magana, kuma ya ga hakan a aikace.

3694302

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha