IQNA

Bayar Da Horo Ga Malamai Da Limamai A Kasar Saliyo

20:56 - March 03, 2018
Lambar Labari: 3482449
Bangaren kasa da kasa, an bude wani shiri na bayar da horo ga malamai da limaman masallatai a kasar saliyo.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran ne ya dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan shiri na bayar da horo.

Wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da irin wanna shiri, wanda shugaban karamin ofishin jakadancin Iran Maisami Zadeh ya samu halarta bude taron, kamar yadda shi ma shugaban jami'ar Almustafa ya gabatar da nasa jawabai a wurin.

Babbar manufar gudanar da wannan shiri dai shi ne bayar da horo ga malamai  a kan mahanga ta ilimim ahlul bait (AS) inda aka gabatar da jawabai a kan wannan mahanga.

Limamai da malamai 30 suke samun halartar shirin, wanda daga karshe kuma za a bayar da kyautuka na girmamawa a gare su.

3696122

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha