IQNA

Jami’an Tasron Kasar Iraki Sun Kame Wasu ‘Yan Ta’adda 20

23:11 - March 26, 2018
Lambar Labari: 3482513
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Iraki sun kame wasu ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyar daesh a cikin lardin Nainawa.

 

Kamfanin dillancin labaran Nainawa ya nakalto daga shafin nashra cewa, jami’an tsaron kasar Iraki sun kame wasu ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyar daesh a cikin lardin Nainawa da suke kokarin kaddamar da hare-haren ta’addanci a yankin.

An kame wadannan mutane su 20 bayan samun bayan sirri a kan hankoron da suke yi wanda ya bayar da dama ga mutanen yankin suka gano su.

Bisa dokar yaki da ta’addanci mai lamba 1/4 za a gurfanar da wadannan mutane domin yanke musu hukunci.

3701906

 

 

 

 

 

captcha