Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sis.gov.eg cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ce ta shirya wa masu gudanar da gasar wannan yawon bude ido.
Daga cikin muhimman wuraren da masu gasa suka ziyarta har da ahram da kuma masallacin Amru bin Al-as, gami da wasu fitattun wurare na tarihi da suke a kasar ta Masar.
Masu gudanar da gasar sun bayyana wannan gasar da cewa ta sha banban da sauran wadanda suka gabace ta, domin ziyaratar wuraren tarihin da suka yi a wannan karo ya banbanta ta da sauran tarukan gasa da suka yi a kasar.
Kasar Masar dai na daga cikin kasashen musulmi da suke da wuraren tarihi da suke da alaka da dubban shekaru.
A gobe Alhamis ne za a gudanar da taron karshe na rufe gasar, wadda ta samu halartar makaranta da mahardata daga kasashe 50 na duniya.