IQNA

An Girmama Daya Daga Cikin Matan Da Suka Nuna Kwazo A Gasar Kur’ani Ta Masar

23:47 - April 05, 2018
2
Lambar Labari: 3482542
Bangaren kasa da kasa, gwamnan lardin Minya a kasar Masar ya girmama yarinyar da ta zo ta hudu a gasar kur’ani ta duniya da aka gudanar a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Yaum Sabi cewa, Isam Albadiwi gwamnan lardin Minya na kasar Masar, ya girmama Tasnin Muhammad Muhammad Abdulaziz ‘yar asalin lardin na Minya, wadda ta zo a matsayi na hudu a gasar hardar kur’ani ta duniya da aka gudanar a kasar.

Gwamnan lardin Minya ya bayar da kyautar wani allo na girmamawa ga Tasnim, haka nan kuma ya bayar da kyautar kudade gare ta, domin jinjina irin kokarin da ta yi a gasar.

Ya ce ko shakka babu kur’ani mai tsarki yana da babban tasirin wajen samar da tsari, kyawawan dabiu, gyaran zukata, gyara rayuwar al’umma ta zamatakwa, da dai sauran abubuwa da dan adam yake bukata na gyaran rayuwarsa da yi mata tsari mai kyau, baya ga haka kuma bin wannan sari nasa shi ne rabauta ta duniya da lahira.

An kammala gasar kur’ani ta kasar Masar ne a wannan mako, gasar da ta samu halartar makaranta da mahardata daga kashen daga kasashen duniya hamsin.

3703281

 

Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
ABUBAKAR ABDULLAHI GWARMAI
0
0
Allah yasalawa kasar masar da alheri da takeyin wanna gasar karatun na alqura"ani na kasa da lasa sabo da tana hada kan musulmi na duniya dama musulmi dan uwan musumine a ko inna yake a duniya
ABUBAKAR ABDULLAHI GWARMAI
0
0
Allah yasalawa kasar masar da alheri da takeyin wanna gasar karatun na alqura"ani na kasa da lasa sabo da tana hada kan musulmi na duniya dama musulmi dan uwan musumine a ko inna yake a duniya
captcha