
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar al-alam cewa, a wata zantawa ta wayar tarho da sheikh Zakzaky ya yi da dansa daga inda ake tsare da shi, ya bayyana cewa Saudiyya ce ta dauki nauyin dukkanin abin da ya faru na kisan gilla a Zaria da ma abubuwan da suka faru kan mabiya Harkar Musulunci daga bayan kisan gillar zaria.
Sheikh Zakzaky ya ce masarautar Saudiyya tana zartar da abin da iyayen gidanta suka yi umarni ne, domin ta biya da kudinta, domin ita kawai ana bata umarnin ta bayar da kudi ne kawai domin a aiwatar, su kuma wadanda suka sanya a yi su ne Amurka da Birtaniya, wadanda suka aiwatar kuma su ne wadanda Saudiyya ta ba kudi domin su yi abin da suka yi.
Sheikh Zazaky dai yana fama da matsalar hawan jinni da kuma rashin gani da idonsa guda, sakamakon harbin da bindiga da sojoji suka yi masa a kan idon nasa a lokacin da suka kai farmaki a gidansa, bayan kasha daruruwa daga cikin mabiyansa a karshen 2015.