IQNA

23:55 - May 11, 2018
Lambar Labari: 3482649

An Tarwatsa Wasu Manyan Wuraren Buyar ‘Yan Daesh A Iraki

Rundunar sojin kasar Iraki ta sanar da rusa wasu manyan wuraren buyar ‘yan ta’addan Daesh a cikin lardin Samirra da ke arewacin kasar.

An Tarwatsa Wasu Manyan Wuraren Buyar ‘Yan Daesh A Iraki

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar sojin Iran Yahya Rasul ya sanar da cewa, sun fara kaddamar da farmakin ne a yankunan Pishgan da Tal Zahab a cikin lardin Samirra.

Ya ce sun samu nasarar rusa wasu muhimman wuraren buyar ‘yan ta’adda guda biyu da suke a wurin, kuma an kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan, yayin sauran kuma suka mika kansu.

Wannan farmaki dai ya zo ne sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ‘yan ta’addan Daesh suka kaddamar a wasu yankuna na Iraki, kamar yadda kuma ake zaton cewa ‘yan ta’addan za su zafafa hare-harensu a cikin ‘yan kwanakin nan domin kawo cikas ga zaben da za a gudanar a kasar.

3713142

 

 

 

captcha