Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran reuters cewa, jami'an 'yan sanda sun samu wani buhu da aka ajiye a kusa da wani masallaci a garin Durban na Afirka ta kudu, wanda ake zaton cewa bam ne.
Jami'an tsaron sun ce an bukaci jama'a da su kaurace wa wurin domin masana kan harkokin abubuwan masu fashewa su gudaar da bincike.
Wannan dais hi ne karon farko da aka kaddamar da farmaki a kan masallacin mabiya mazhabar shi'a akasar Afirka ta kudu, duk da cewa dai har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin hakan, amma dai ana nuna yatsun tuhuma akan kungiyoyin wahabiyawa masu masu tsatsauran ra'ayi.
A ranar Alhamis da ta gabata ce wasu mutane uku suka kutsa kai cikin masallacin, inda suka yi ta daba ma mutane wuka, sun kasha mutum daya sun kua jikkata wasu biyu.