Bangaren kasa da kasa, an watsa karatun kur’ani mai sarki kai tsaye da ake gudanawa tare da halartar jagora a kowane farkon watan Ramadan a tashoshin talabijin na kur’an da Alamanr.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau ne ake gudanar da karatun kur’ani tare da halartar jagora kamar yadda aka saa a kowace shekara a ranar farko ta watan Ramadan.
A wannan shekarar ana watsa shirin ne kai tsaye a tashoshin talabijin na Kur’ani da kuma Amanar da kuma tashar Ma’arif.
A kowace shekara dai al’umma na taruwa a gidan jagora Ayatollah Sayyid Ali Khamenei domin karatun kur’ania farko watan Ramadan domin samun albarkacin watan.