IQNA

Za A Bayar Da Shahadar Digiri Ga Mahardata Kur’ani A Sudan

23:31 - June 05, 2018
Lambar Labari: 3482728
Bangaren kasa da kasa, sheikh Ibrahim Sunusi mataimakin shugaban kasar Sudan ya bayyana cewa shugaban kasar zai bayar da digiri ga dukkanin mahardata kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Al-raya cewa, mataimakin shugaban kasar Sudan ya bayyana cewa shugaban kasar zai bayar da digiri ga dukkanin mahardata kur’ani domin girmama su.

Ya ci gaba da cewa shugaban na Sudan ya yank wannan shawara n da nufin ganin an dago da matsayin kur’ani ta hanyar girmama mahardatansa a kasar.

Ya kara da cewa hakan zai zama wata hanya ce ta kara karfafa gwiwar mahardatan da kuma wadanda suke da niyyar hardace kur’ani.

3720568

 

 

 

 

captcha