Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, a jiya ne aka girmama mahardata kur’ani mai tsarki su 120 a yankin Tursina na kasar Masar bayan da suka nuna kwazoa wata gasar kur’ani ta yankin.
Bayanin ya ci gaba da cewa, an gudanar da wannan gasar ne a dukkanin bangarori na hardar kur’ani mai sarki, kama daga hardar dukkanin ur’ani da kuma rabi da kuma rubi.
Baya ga haka kuma dukkanin yara da shekarunsu ke kasa da 6 da suka shiga cikin wannan gasa an ba su kyautuka na musamman, domin kara karfafa gwiwarsu a kan lamarin kur’ani.